Shop information for magajinwilbafos.org.ng - My Lead Fox

magajinwilbafos.org.ng

https://magajinwilbafos.org.ng

Yarima yayi murmushi a lokaci na farko tun bayan fara taron. Ya kalli Dul'Ururu na ɗan lokaci sannan ya ɗauke kai ba tare da yace komai ba.Waziri ya dakko takarda ya rubuta dukkan abubuwan da aka tattauna zuwa yanzu. Maruta zai jagoranci Ashura su kashe tawagar matattu da rayayyu. A lokaci guda zasu kare doron ƙasa ta farko. Shi kuma Waziri da Dul'Ururu zasu kashe Taidara. Yarima kuma zai je ya kashe 'irin' da Taidara ya shuka, koma mai Hakan yake nufi. Har yanzu dai akwai abinda basu tattauna ba.Wane mataki zamu ɗauka akan Armad daya shigo doron ƙasa ta farko, sannan kuma a halin yanzu wane mataki zamu ɗauka akan iyalan Maikiro'Abbas da suka kashe mana mutane da kuma Rafiyan Nazara da yake neman kwace Rafiya?Yarima ya kada kafada yace, Ba jimawa za'a naɗa Rabi sarauniya a ƙasar maikironomada. Sannan kuma za'a naɗa Nazara a matsayin sarki a ƙasar Rafiya. Idan hakan ta faru sai a tura yara su kai musu ziyara. Amsar da zasu bayar a lokacin ita zata zamar musu hukunci. Abu guda shi ne wannan garuruwa nasu basu da muhimmanci a yaƙi mai zuwa. Taidara bazai ɗauko gama-garin mayaka na daular Rafiya ko maikironomada ya taho dasu yaƙi ba. Sannan kuma bashi da lokacin da zai yi amfani da daular ya gina wasu mayakan, lokaci ya kure masa. Saboda haka basu daular a wannan lokaci bazai canja komai ba. Daɗin dadawa idan muka kai hari daular Rafiya ko maikironomada muka kashe gama-garin mutane, hakan babu abinda zai yi sai ƙarawa Taidara da Wilbafos ƙarfi da farin jini a yaƙin da zai zo. Kada ku manta har yanzu mutane suna ɓangaren Ururu. Mafi yawan mutane basu da matsala da jinzidal ko Amri. Duk wannan rigima da Wilbafos suke yi akan karya rukunan addinin mu, iyakacin su kaɗai ne da abokan su. Idan zai yiwu, ina so abin ya zauna a haka. Addinin jinzidal addini ne na zaman lafiya.Shi kuma Armad… Yarima ya ɗan yi shiru cikin tunani kafin ya juya wajen ɗan sakon daya kawo labarin Armad. Shi kaɗai ya shigo?A'a, mai girma yarima, da shi da Nusi Kil'zanki suka shigo, inji ɗan sakon.Yarima ya ɗan yamutse fuska kafin ya fashe da dariya ya juya gefe yace, Dul'Ururu, kace a ƙarshe da Armad da Nusi ne suka tsaya, ko?Dul'Ururu ya gyada kai, lamarin da ya ƙara jefa yarima cikin tunani. Yasan tabbas akwai wata alaƙa tsakanin zuwan su Armad doron ƙasa ta farko da kuma kammala yaƙin da akai, to amma kuma ya kasa gano alaƙar.Bayan ɗan lokaci yayi murmushi yace, Kuyi ƙoƙarin neman su, amma kada ku damu kan ku da yawa akan al'amarin yara. Idan sun bayyana kan su sai kuyi musu duk hukuncin da rukunin Amri ya tanada. Shike nan.Nan take kowa ya amince da wannan shawara. Yadda suka ɗauki lokaci suna magana akan Taidara, basu ɗauki lokaci suna magana akan Armad haka ba. Kai kace basu da lokacin batawa akan sa.Ba jimawa wannan majalisi yazo ƙarshe.A dai-dai wannan lokaci da majalisin Ururu suka yanke shawara akan abinda zasu aikata na gaba, a dai-dai lokacin Armad ne yake zaune acikin wani katon gida. Ɗaure a gabansa wani mutum ne kakkaura. Idanun mutumin bakake ne samfurin Ururu. Armad kuma yana zaune akan teburi da alkalami a hannunsa. Idan ka lura sosai zaka ga jini ne yake zubowa ta idanun mutumin da bakinsa.Bayan ɗan lokaci, Armad yaja numfashi tare da girgiza kai yace, Na fuskanta. Ku shigo dana gaba.Yana rufe baki, kofar dakin ta buɗe. Mutun-mutumin Armad ya shigo da wani mutumin mai idanun Ururu dakin. Da sauri ya kwance ɗayan mutumin dake zubar da jini ta ido sannan ya daura ɗayan a jikin kujerar. Bayan ya tabbatar komai ya ɗauru sai ya ɗauki gawar ɗaya mutumin ya fita da ita.Kada kaji tsoro, Armad ya gayawa mutumin da aka shigo dashi. Ɗan bincike kawai nake yi akan jinsin ku. Idan ba matsala aka samu ba to tabbas zaka fita da kafafun ka.Mutumin ya yamutse fuska cikin takaici. Ya rasa kuka zai yi ko dariya. To amma bashi da iko akan jikin sa. Bai san wane tsafi wannan mutum dake gabansa mai fararen idanu yayi amfani dashi ba, to amma tabbas bazai iya guduwa ba. Bayan ɗan tunani ya yanke shawara ya miƙa wuya. Watakila ya tsira da ransa. Mai kake so ka sani? Ya tambayi Armad.Jin tambayar yasa Armad yayi murmushi. Yasan wannan zai bashi haɗin kai. Kayi dabara, inji Armad. Bazan ɓoye maka ba, ni Wilbafos ne. Kuma alaƙar dake tsakanin ƙabilar ka da tawa ba mai kyau bace. Saboda haka ina bincike ne akan yadda kuke anfani da izza. Idan ka amsa min kowace tambaya dai-dai to nayi alƙawarin zaka tsira da ranka.Armad ya ɗan ƙura masa ido domin ya tabbatar ya fuskance shi. Sannan yaci gaba, Ya sunan ka?Suna na Hani Ururu.Da kyau. Haka nake so duk wata tambaya da zanyi maka ka amsa ta da wuri ba tare da ka bata min lokaci ba. Meye abu na farko daka fara koya a fannin izza?Farkar da idanuna na Ururu, inji Hani.Armad ya gyada kai. Mutumin daya fita ma abinda ya faɗa kenan. Daga nan fa?Sai nayi amfani da izzar dake cikin idanun na fara koyon fasahohin farko.Idan Ururu yace maka 'fasahohin farko' to yana nufin fasaha huɗu na Ururu wato saɓani, hakika, bayani, da shankil.Daga nan fa?Sai na zaɓi fasahar takobi aka saka ni a karkashin malami na fara koyon darasi.

Keywords:

Category:

City:

State:

Country: Nigeria (NG)

Currency :

Avg product price:

Platform: WooCommerce

Technologies used: Facebook SDK, Google Adsense, Google Analytics, Google Tag Manager

Contact page: https://magajinwilbafos.org.ng/contact-us

Get Email Get Phone
Signup for Free. No Credit Card required.

Find WooCommerce stores worldwide and make them your client.

  • Find more shops on WooCommerce in Nigeria.
  • Find e-commerce stores worldwide and make them your client.

  • Find more shops on e-commerce in Nigeria.

  • < Previous Shop 7,862,817 of 10,181,674 Next >

    Get started with a simple yet powerful solution for acquiring leads?

    Suitable for marketing agencies, app developers and new business ideas.

    No credit card required.

    REF: 6466979